Sarkin Bichi Alhaji Nasir Ado Bayero

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Sarkin Bichi Alhaji Nasir Ado Bayero



Mai Martaba Sarkin Bichi
Alhaji Nasir Ado Bayero
Hoto:  https://technext.com


Gabatarwa

Mai Martaba Sakin Bichi, Alhaji Nasir Ado Bayero, shi ne ɗa na uku a wajen Marigayi Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji (Dr) Ado Bayero. Gogaggen basarake ne ta hanyar gado da kuma koyo; fitaccen ɗan kasuwa, sannan kuma hamshaƙin attajiri. Mutum ne mai matuƙar biyayya, haƙuri, gaskiya, riƙon amana da kuma kyautata wa jama’a.

Ya gaji sarauta daga dukkan ɓangarorin mahaifansa biyu; mahaifi da kuma mahaifiya. Mahaifinsa, Marigayi Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji (Dr) Ado Bayero, sarki ne ɗan sarki kuma jikan sarki. Mahaifiyarsa kuma ‘yar sarki ce sannan jikar sarki a Ilorin ta Jahar Kwara. Sannu a hankali cikin wannan rubutu, mai karatu zai tabbatar da gaskiyar lamari.

Haihuwa

An haifi Mai Martaba Sarki, Alhaji Nasir Ado Bayero a Gidan Rumfa; Fadar Masarautar Kano a ranar 2 ga watan Fabarairun shekarar 1964.

Salsala

Mai Martaba Sarkin Bichi, Alhaji Nasir Ado Bayero, zuriyar gidan malam Ibrahim Dabo ne ta ɓangaren Marigayi Sarkin Kano Alhaji (Dr.) Ado Bayero.

Shi ɗa ne ga Alhaji Ado Bayero, sarkin kano na goma sha uku a cikin sarakunan Fulani, shi kuma ɗan Alhaji Abdullahi Bayero, sarkin Kano na goma a cikin jerin sarakunan Fulani, shi kuma ɗan Sarkin Kano Muhammadu Abbas, sarki na takwas a cikin jerin sarakunan Fulani, shi kuma ɗan Abdullahi Maje Karofi, sarkin Kano na huɗu a cikin jerin sarakunan Fulani, shi kuma ɗan Malam Ibrahim Dabo, sarki na biyu a cikin jerin sarakunan Fulani sannan kuma ɗaya daga cikin waɗanda suka karɓo tutar jahadi daga Shehu Usmanu Ɗanfodiye zuwa Kano tare da kafa ta a Kano.

Haka nan ta ɓangaren mahaifiyarsa, Mai Martaba Sarkin Bichi jika ne ga Mai Martaba Sakin Ilorin.


Mai Martaba Sarkin Bichi
Alhaji Nasir Ado Bayero yana jawabi
Hoto:  Twitter: hrh_nasir_ado_bayero

Karatu

  • Alhaji Nasir Ado Bayero ya yi karatun firamare da sikandire a Kano (Levene, 2019).
  • Ya yi Karatun digirin farko a fannin aikin jarida (Mass communication) a jami’ar Maiduguri, ya kammala a shekarar 1987, (Akinpelu, 2018).
  • Ya samu horo na Musamman a Tsangayar Kasuwanci na Gawurtacciyar Jami’ar Harvard da Ƙasar Amurka (PRNigeria, 2020).
  • Ya halarci kwas na koyon harshen Jamusanci a shekarar 1993, (Akinpelu, 2018).

Gagayyar Aiki

  • Ma'aikacin Continental Merchant Bank 1988 - 1989.
  • Ma'aikaci a Kamfanin Hada-Hadar Albarkatun Mai, Coastal Corporation da ke garin Houston a Jahar Texas, Amurka. 1990 - 1991.
  • Ma'aikaci a Kamfanin Hamlet Investment, Inc, da ke Ingila 1991 - 1992.
  • Mamba na Hukumar Daraktocin Kamfanin Intel Services Nigeria Limited, kamfanin fito (Dakon kaya daga ƙasashen ƙetare zuwa Najeriya da fitarwa) mafi girma a Najeriya.
  • Mamba na Hukumar Daraktocin Kamfanin Barton Bay Nigeria Limited.
  • Mamba na Hukumar Daraktocin Masaukin Baƙi na Sophitel Abuja.
  • Mamba na Hukumar Gudanarwar Leverage Insurance Brokers limited.
  • Mamba na Kwamatin Amintattu na Jami'ar Admiralty University of Nigeria da ke Jahar Delta.
  • Shugaban Daraktocin Kamfanin Sadarwa na 9mobile.
  • Mamba a Hukumar Daraktocin SEPLAT, kamfanin hada-hadar albarkatun mai a Najeriya.
  • Mataimakin Shugaban Kamfanin Levene Energy group.

Gogayyar Sarauta

Alhaji Nasir Ado Bayero ya riƙe muƙaman sarauta kamar haka:

  • Hakimin Nassarawa.
  • Turakin Kano, Hakimin Nassarawa.
  • Chiroman Kano, Hakimin Nassarawa.

Sarkin Bichi

Alhaji Nasir Ado Bayero, tsohon Chiroman Kano, ya zama sarkin Bichi na biyu a ranar Litinin 9 ga watan Maris na shekarar 2020 kamar yadda Yusuf (2020) ya ruwaito kuma aka wallafa a shafin Internet na Jaridar Premium Times.

Naɗin nasa ya biyo bayan ciyar da likafar Mai Martaba Sarkin Bichi na farko gaba, Alhaji Aminu Ado Bayero, wanda yake kuma ɗan’uwa ne ga shi Mai Martaba Sabon Sakin Bichi.


Mai Martaba Sarkin Bichi
Alhaji Nasir Ado Bayero yana jawabi
Hoto:  Twitter: hrh_nasir_ado_bayero

Manazarta:


Akinpelu O. (2018). Meet Nasiru Ado Bayero, the New Chairman of 9Mobile. An ciro a shekarar 2020 daga shafin: https://technext.ng/2018/11/13/meet-nasiru-ado-bayero-the-new-chairman-of-9mobile/

Jami'ar Admiralty (2020). HRH Nasir Ado Bayero. An ciro a shekarar 2020 daga shafin: https://adun.edu.ng/about-us/board-of-trustees/hrh-nasir-ado-bayero/

Levene Energy Group (2020). HRH Nasir Ado Bayero Group Vice Chairman. An ciro a shekarar 2020 daga shafin: https://www.leveneenergy.com/our-key-people/hrh-nasir-ado-bayero-group-ɓice-chairman/

Nasir J. (2020). Profile: Ado Bayero, the mass communication graduate who ‘never begged’ for titles. An ciro a shekarar 2020 daga shafin: https://www.thecable.ng/profile-ado-bayero-the-mass-communication-graduate-who-never-begged-for-titles

PRNigeria (2020). Bayero’s Sons, Aminu and Nasiru Become Emirs of Two Emirates in Kano. An ciro a shekarar 2020 daga shafin: https://prnigeria.com/2020/03/09/aminu-nasiru-emirs-kano/

Yusuf K. (2020). Ganduje appoints Nasiru Ado Bayero new Emir of Bichi. An ciro a shekarar 2020 daga shafin: https://www.premiumtimesng.com/regional/nwest/381025-ganduje-appoints-nasiru-ado-bayero-new-emir-of-bichi.html

Sarakuna


Kasuwanni


Bukukuwa


Wasu Gurare


Yaƙuƙuwa


Ƙofofin Bichi


Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:

       

Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub